25 Disamba 2014 - 12:23
Isi, sun tabka asara mai yawa a garin Alanbar da salahuddin.

Sojojin Iraki sun yima yan ta'adda na kungiyar Da'ish mumunar asara a garuruwan falluja, takrid,yasrab da diyala,inda suka halaka da yawa na yan kungiyar. Ruhotanin suna nuni da cewa yan ta'addan sun firgita yayin da sojojin kwannati da kuma yan sa kai sukai masu kofar raggo.

Tashar labarai ta irinn tace;  a hare-haren da sojojin suka kai a garuruwan falluja da alanbar yayi sanadiya hallaka ya ta'adda da dama.

A wani bangaren jami'an tsaro na Iraki sun kare harin da yan ta'adda suka kai na alrimadi ance yan ta'addan suna shigowane daga syria wadda itama ke fama da yaki da yan kungiyar Da'ish.

A gefe daya kuma ministan tsaro na Iraki ya shelanta yanto dukkanin wani yanki wanda yan ta'addan suka kama, yace hakan zata faru ne yayin da kabilun garuruwan da abun ya shafa suka bada koyan baya da kuma daukar makamai.ABNA